Shugabannin mulkin sojan Nijar, sun bukaci shugaban ofishin jakadancin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ya fice cikin sa’o’i 72.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Afirka ta Yamma ta fitar, ta zargi Majalisar Dinkin Duniya da yin amfani da manaƙisar Faransa wajen hana ƙasar shiga babban taron Majalisar Dinkin Duniya a watan da ya gabata, da kuma sauran tarukan ƙasashe.
Gwamnatin mulkin sojan da ta hamɓarar da mulkin dimokradiyyar Nijar a watan Yuli, ta kuma kori sojoji da jakadan Faransa