A yau ne Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago, Joe Ajaero, zai amsa gayyatar ƴan sanda domin amsa wasu tambayoyi game da zarginsa da ɗaukar nauyin ta’addanci da laifukan kafofin sadarwa da cin amanar ƙasa da sauransu.
A ranar Talatar ta da gabata ne wato 20 ga watan Agusta ƴan sandan suka gayyaci shi ya bayyana a gabansu bayan wani samame da suka kai a sakatariyar NLC da ke Abuja.
Amma shugaban NLC ɗin ya bayyana cewa zai mutunta gayyatar a ranar Alhamis, 29 ga watan Agustan, maimakon ranar da ƴansandan suka buƙata da farko.
“Ƴan sandan sun ce sun yi samamen ne domin gano wasu muhimman abubuwa da suke da alaƙa da zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi a Najeriya,”
Domin nuna goyon baya ga Ajaero, Ƙungiyar Ƙwadago ta umarci mambobinta a faɗin ƙasar da su taru a hedkwatar ƴan sanda na jihohinsu, “har sai shugabansu ya bar hedkwatar ƴan sandan.”
Ƙungiyar Ƙwadagon dai a makon da ya gabata ta yi gargaɗi tare da yin barazanar fara yajin aikin sai baba-ta-gani, idan har aka kama shugabanta, Joe Ajaero.
Idan ba a manta ba, dubban mutane ne suka fito suka yi zanga-zangar matsin rayuwa, ƙarƙashin jagorancin wata ƙungiya mai suna Coalition of Concerned Nigerian Citizens.