fidelitybank

Shugaban NLC bai amsa gayyatar ‘yansanda ba

Date:

Shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa zai mutunta gayyatar da rundunar ‘yan sanda ta yi masa a ranar Laraba 29 ga watan Agustan 2024, maimakon yau Talata 20 ga watan Agustan 2024 kamar yadda aka buƙata tun farko.

A cikin wata wasiƙa da shugaban ƙwadagon ya aika wa ƴansanda ta hannun lauyoyinsa, Ajaero ya bayyana cewa, wasikar gayyatar ta same shi ne a jiya Litinin, kuma shugaban yana da wasu ayyukan da ya tsara gudanarwa a yau Talata.

Sai dai sanarwar ta ce Ajaero a shirye yake ya amsa gayyatar a ranar Laraba.

Bugu da kari, Ajaero ya buƙaci ƴansanda da su bayar da cikakkun bayanai game da zargin da ake yi masa, waɗanda suka haɗa da samar da kuɗaɗen tallafa wa ayyukan ta’addanci da haɗa baki wajen aikata laifuffuka da cin amanar ƙasa, da kuma aikata laifuka ta shafukan intanet.

Wasiƙar ta ambato sashe na 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bai wa wanda ake tuhuma ƴancin samun cikakken bayani game da yanayi da takamaiman zarge-zargen da ake yi masa.

nigerian 
newspapers today the sun

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp