Hage Geingob, Shugaban Namibia ya mutu.
Geingob ya mutu da sanyin safiyar Lahadi bayan ya yi fama da cutar kansa.
An sanar da mutuwar dan shekaru 82 a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban kasar Nangolo Mbumba.
“A cikin tsananin bakin ciki da nadama na sanar da ku cewa Allah ya yi wa masoyinmu Dr. Hage G. Geingob, shugaban kasar Namibiya ya mutu a yau.
“A gefensa akwai masoyiyar matarsa Madame Monica Geingos da ‘ya’yansa.”