Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kwara, Hon. Olawoyin Magaji ya rasu.
An rahoto cewa Olawoyin mai shekaru 57 ya mutu bayan gajeruwar rashin lafiya.
Marigayi shugaban majalisar ya wakilci mazabar Ilorin ta tsakiya a kan tikitin jamâiyyar APC mai mulki, kuma yana da burin sake tsayawa takara karo na biyu a zaben 2023 mai zuwa.
Kakakin Kakakin Majalisar, Mista Funsho ya kasa samunsa har zuwa lokacin hada wannan rahoto a safiyar ranar Litinin.