Shugaban ƙasar Malawi, Lazarus Chakwera ya dakatar yin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare.
Haka kuma ya ɗauki makamancin wannan mataki kan ministoci da jami’an gwamnatinsa a wani yunƙuri na rage kashe kuɗin gwamnati.
Matakin na zuwa ne sakamakon karyewar darajar kudin ƙasar, yayin da ƙasar ta samu bashi daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF domin bunƙasa tattalin arzikinta.
Mista Chakwera, ya kuma umarci duka ministocinsa da yanzu haka ke ƙasashen waje da su koma cikin ƙasar.
An kuma rage alawus ɗin man fetur da ake bai wa manyan jami’an gwamnati da kashi 50.
Tattalin arzikin Malawi na cikin mawuyacin hali da ya haɗa da karancin man fetur da iskar gas, da kuma matsalar hauhawar farashin kayyaki.