fidelitybank

Shugaban majalisu ku bayyana mana kuɗaɗen gudanarwar ku na wata-wata kowa ya sani – SERAP

Date:

Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a ƙssar nan, ta buƙaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas su bayyana ”haƙiƙanin kuɗin gudanarwar” da ake bai wa mambobin majalisun biyu a kowane wata.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi ta buƙaci shugabannin majalisun biyu su bayyana mata cikakkun bayanan kuɗin da majalisun biyu ke kashewa a matsayin kuɗin gudanarwa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan ƙasar ke ci gaba da tafka muhawara kan yawan kuɗin gudanarwa da ake bai wa ‘yan majalisar dokokin ƙasar a kowane wata.

A makon da ya gabata ne tsohon shugaban ƙasar, Olusegun Obasanjo ya zargi ‘yan majalisar da yanka wa kansu albashi da alawus -alawus a ƙasar.

Lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin ‘yan ƙasar, inda har wasu ‘yan majalisar dokokin ƙasar suka bayyana abin da ake biyansu.

Ko a makon da ya kamata ma, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila daga jihar Kano, ya shaida wa BBC cewa ana biyansa naira miliyan 21 a kowane wata a matsayin kuɗin gudanarwar ofishinsa.

Yayin da ya ce yana karɓar albashin da bai kai naira miliyan guda ba a kowane wata.

Ƙungiyar ta Serap ta kuma yi kira ga jagororin majalisar dokokin ƙasar su dakatar da yanka wa kansu albashi da alawu-alawus da sunan kuɗin gudanarwar, kamar yadda aka yi zargi.

Haka kuma ƙungiyar ta kira da a daina sanya wa ‘yan majalisar kuɗin gudanarwar da ake zargi cikin asusun ajiyarsu na banki, kai tsaye, bayan da ta yi zargin cewa suna amfani da kuɗin ta hanyar da ba ta dace ba.

Tana mai cewa rashin sanya kuɗin a asusun ‘yan majalisun zai bai wa hukumomin yaƙi da cin hanci damar gudanar da bincike idan buƙatar hakan ta taso.

sahara hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp