Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar ta’aziyya ofishin jakdancin Najeriya da ke birnin Monrovia domin jajanta rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Yayin ziyarar tasa a ranar Laraba, Mista Boakai ya sanya hannu kan rajistar makoki a ofishin bayan ya samu tarɓa daga jakadan Najeriya R.O Mohammed.
Alaƙar Najeriya da Laberiya na da tarihi sosai. A shekarun 1990, Najeriya ta tura sojojinta domin kawo ƙarsen yaƙin basasar ƙasar.