Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya sanar da ƙara yawan mafi ƙarancin albashi a yau Lahadi da kashi 12 cikin 100 yayin da gwamnatinsa ke yaƙar tsadar rayuwa a ƙasar.
Hauhawar farashi ta kai matakin da ba ta taɓa kaiwa ba cikin wata bakwai a watan Afrilu, akasari saboda tashin farashin mai da kayayyakin abinci, in ji hukumomi.
“A matsayinmu na gwamnati mai tausayi, muin lura cewa akwai buƙatar ƙara albashi mai ƙarfi don kare ma’aikatanmu daga shiga wani ƙuncin,” a cewar Kenyatta yayin jawabin Ranar Ma’aikata.
Ya ce ƙarin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayu, inda zai tashi daga kuɗin Kenya shilling 13,500 duk wata (dala 116 kenan) zuwa 15,120 (dala 130.5).
Sai dai kuma ƙarin bai kai abin da ƙungiyar ƙwadago ta Central Organisation of Trade Unions-Kenya (COTU) ta nema ba na kashi 24 cikin 100.