Mataimakin firaministan Slovakia, Robert Kalinak, ya ce ana sa ran firaministan ƙasar, Robert Fico ”zai samu sauƙi” bayan ƙarin tiyatar da likitoci suka yi masa
Robert Fico, mai shekara 59, ya samu munanan raunuka bayan harbi da wani mutum ya yi masa a garin Handlova ranar Laraba.
Jami’ai sun ce ba zai yiwu a mayar da shi Bratislava, babban birnin ƙasar cikin kwanaki masu zuwa ba.
An gurfanar da mutumin da ya yi yunƙurin kashe shin a gaban kotu.
Mai magana da yawun kotun ta ce za a ci gaba da tsare shi har zuwa ƙarshen shari’ar da ake yi masa.
Mataimakin firaministan ya ce mista Fico na samun sauƙidaga raunukan da ya ji, kuma babu buƙatar naɗa mai riƙon ƙwarya don jagorantar gwamnati