Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro, ya tsere zuwa Florida maimakon zuwa bikin mika mulki ga shugaban da ya ci zabe Lui Inacio Lula da Silva, mai sassaucin ra’ayi.
Dan siyasar mai ra’ayin rikau ya isa Orlando ne a Florida a safiyar ranar Asabar a jirgin sojin saman Brazil, in ji rahotanni.
Ya fice daga kasar ne bayan aikewa da sakon bankwana ga magoya bayansa, inda ya ce har yanzu yana kan bakarsa ta cewa akwai lamba da zaben da aka yi, ya kuma soki duk wata zanga-zangar tashin hankali da za a yi da sunan kin amincewa da sakamakon zaben da aka yi.
Bolsonaro ya yi alkawarin cewa ba zai halarci mika mulki da bikin rantsuwa ga Lula da zai gudana a ranar Lahadi.
Mataimakin shugaban kasar Hamilton Mourao, shi ne zai yi zama a matsayin shugaban har zuwa ranar karshe a ofis, ko da yake dama ya ce ba zai halarci bikinba tun a watannin baya.