Shugaban karamar hukumar Ungogo a Jihar Kano, a kokarinsa ya tallafa wa iyaye marasa galihu da ke fama da matsalar kasa biyan kudin jarabawa, inda ya raba sama da Naira miliyan 22 ga dalibai marasa galihu 1,000 domin samun damar yin rijistar shiga Hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO).
Da yake bayyana hakan a ranar Talata, Shugaban Majalisar, Engr. Abdullahi Garba Ramat ya sanar da hakan ne a yayin bikin raba kudaden ga wadanda suka amfana a karshen mako a sakatariyar majalisar da ke jihar Kano.
Ya ce gwamnatin jihar ta tallafa wa hukumar da biyan dalibai kusan 200 ne yayin da karamar hukumar ta yi wa wasu dalibai 800 birki.
A cewar sa, an yi hakan ne domin rage wa iyaye nauyin biyan kudin jarabawa tare da inganta harkar ilimi a karamar hukumar.