Sabon shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Karasuwa a jihar Yobe, Hon. Lawan Gana, ya rasu ranar Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa, Gana ya rasu ne a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Nguru bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Wannan na zuwa ne yayin da za a rantsar da dukkan kwamitocin riko na LG guda 17 a ranar Juma’a da Gwamna Mai Mala Buni ya yi.
A tsakanin shekarar 2023 zuwa 2007, an zabi marigayin a matsayin dan majalisar dokokin jihar Yobe mai wakiltar karamar hukumar Karasuwa a karkashin jam’iyyar PDP.
Ya kuma kasance mataimakin dan takarar gwamna a PDP a 2015, amma ya koma APC a 2019.


