Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Oyo, Honorabul Isaac Ajiboye Omodewu ya rasu.
Omodewu ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Litinin.
Ya rasu ne a kasar Amurka, inji rahoton DAILY POST.
Omodewu ya rike mukamin kwamishina a lokacin tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi.
Marigayin ya fito ne daga karamar hukumar Itesiwaju a shiyyar Oke Ogun geopolitical zone.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a jihar, Wasiu Olawale Sadare ya tabbatar wa da manema labarai.
Sadare a tattaunawarsa da wakilinmu ta wayar tarho ya ce shugaban ya rasu.
Ya ce, “Shugaban ba ya nan. Gaskiya ne shugaban ba ya nan.
“Ya mutu da sanyin safiyar yau a Amurka.”