Shugaban Jamhuriyar Nigar, Mohamed Bazoum, ya taya sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu murnar cin zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar.
Shugaba Bazoum ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twita, inda ya ce yana taya ‘yan Najeriya murna bisa wannan nasara da kuma jajircewarsu na tabbatar da ci gaban dimokuraɗiyya.
Ya ce nasarar ba ta Najeriya kaɗai ba, amma ga illahirin nahiyar Afirka.