Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya sallami ɗaya daga cikin mataimakansa saboda wata tafiya shaƙatawa zuwa Antarctica da ya yi tare da matarsa Nowruz.
Shugaban ya sallami mataimakin nasa ne saboda abin da ya bayyana da “almubazzaranci” da kuɗi.
Ofishin shugaban ƙasar ya ce tafiya ta mataimakin shugaban ƙasa Shahram Dabiri “ba ta dace ba a daidai lokacin da Iran ke fama da matsain tattalin arziki, kuma ƙasar ba za ta aminta ba.”
An ta yaɗa hotunan Dabiri da matarsa ne suna shaƙatawa a kafofin sadarwa a Iran, inda suka jawo ce-ce-ku-ce da suka a tsakanin al’ummar ƙasar.
Pezeshkian ya ce ya sallami Dabari a matsayin mataimakin shugaban ƙasa mai kula da harkokin majalisa saboda “‘almubazzaranci’ wajen kashe kuɗi, ko da kuwa daga aljihunsa ya ɗauki nauyin zuwa shaƙatawar.
“A gwamnatin da ke bin tafarkin imam na farko na Shia wato Imam Aali, tafiyar da za a kashe maƙudan kuɗi ba ta dace ba ga jami’in gwamnatin ko da kuwa daga aljihunsa ya kashe kuɗin,” in ji Pezeshkian