fidelitybank

Shugaban IPOB ya soki shirin gwamnati na yin shari’a a ɓoye ga ƴan ta’adda

Date:

Jagoran kungiyar ‘yan aware ta IPOB a Kudu maso Gabashin ƙasar nan, Nnamdi Kanu, ya shigar da kara a wata kotun tarayya, yana neman ta soke wani umarni da bangaren shari’a ya fitar a farko wannan watan da ke cewa za a daina sauraren dukkan shari’u na ta’addanci a bainar jama’a.

Nnamdi Kanu ya sanar da kotun ta hanyar lauyoyinsa cewa, umarnin ya taka tsarin mulki da wasu dokokin kasar, kuma ya kamata ta soke shi.

A ranar 8 ga watan nan ne mai shari’a John Terhemba Tsoho ya bayar da umarnin daina sauraren shari’un da ke da alaka da ta’addanci a bainar jama’a domin kiyaye tsaron dukan wadanda ke da alaka da shari’ar.

Alkalin ya hana ‘yan jarida halartar zaman kotunan da ke sauraren irin wadannan shari’un.

Baya ga alkalin da zai saurari shari’ar, mutanen da aka amince musu shiga dakin shari’ar su hada da wasu zababbun ma’aikatan kotun da jami’an tsaro.

Kanu ya musanta aikata wani alifi.

daily sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...

Mukarraban gwamnati ba zan lamunci dabi’ar zubar da kima ta ba – Abba

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargaɗi masu...

WAEC ta sake bude shafinta don duba jarabawar bana

Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta bayyana...

Indonesia za ta gina asibiti dubu biyu ga Falasɗinawa

Indonesia ta sanar da cewa za ta kafa wata...

Lauyan Sowore ya bukaci a sake shi cikin gaggawa

Lauyoyin ffitaccen ɗan gwagwarmayar nan kuma ɗan jarida, Omoyele...

Najeriya da Indiya za su haɗa kai na yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi

Hukumar hana sha da fatauncin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya,...

Jihohi 19 da za a yi kwana 9 a na ruwan sama harda Kano – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen za a shafe kwana...

Tinubu ya mika sakon ta’aziyya bisa rasuwar matar MKO Abiola

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa bisa...

Abubuwan da Kwamiti ya gano a wajen Kwamishina mai murabus na Kano

A ranar Litinin ne kwamitin binciken badaƙalar belin Danwawu,...
X whatsapp