Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe, ya kasance a sansanonin Senegal da Tunisia a ranar Asabar a wani bangare na ziyarar da ya kai kasashen Afirka da ke halartar gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 a Qatar.
Motsepe ya fara wannan rana ne da ziyarar sansanin ‘yan wasan kasar Senegal a dakin wasanni na Handball na Duhail.
Daga nan dan Afirka ta Kudu ya zarce zuwa sansanin Tunisia da ke Wyndham Grand West Bay Beach otal a Doha.
Shugaban na CAF, a cewar bayanai na yanar gizo na CAF, zai kuma ziyarci Morocco, Kamaru da Ghana a cikin kwanaki masu zuwa.
A ranar Lahadi ne za a fara gasar shekara hudu.
Qatar mai masaukin baki za ta kara da Ecuador a wasan farko a filin wasa na Al Bayt mai daukar mutane 60,000 da ke Al Thor.