Likitan Isra’ilar da ya jagoranci gudanar da bincike kan gawar shugaban Hamas Yahya Sinwar, ya ce ya mutu ne sakamakon harbin bindiga a ka.
Da yake magana da kafafen watsa labaran Amurka, Dr Chen Kugel, ya ce ya gano raunuka a wasu sassan jikinsa, ciki har da kafaɗarsa, wanda ya ji sakamakon samunsa da kwanson maƙami mai linzami ya yi.
Ya ce waÉ—annan raunuka sun matukar illata shi sosai, sai dai abun da ya janyo ajalinsa shi ne harbin da aka masa a ka.
Da farko dai rundunar sojin Isra’ila ta ce Yahya Sinwar ya mutu ne sakamakon harbin gidan da yake ciki da tankar yaÆ™in sojoji ta yi.