Shugaban BBC Richard Sharp, ya sanar da yin murabus bayan da wani rahoto ya same shi da laifin saɓa ka’idar aiki.
A wata sanarwa da ya fitar kafin wallafa rahoton, Sharp ya ce Adam Heppinstall KC, wanda ya jagoranci kwamitin binciken, ya karkare cewa “Saɓa ka”idar aiki da nayi kan naɗe-naɗe, ba zai rusa muƙami ba.”
Sharp ya ce, zai yi murabus ne domin kare muradun BBC.
Ya ce zai ci gaba da zama akan muƙaminsa har zuwa karshen watan Yuni lokacin da za a nemi wanda zai maye gurbinsa.