Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, Herbert Hainer, ya nuna shakku kan matakin da dan wasan bayan kungiyar Niklas Sule, ya dauka na barin kungiyar a karshen kwantiraginsa na komawa Borussia Dortmund.
Dortmund ta sanar a ranar Litinin cewa, ta riga ta kulla yarjejeniya da dan wasan baya na Jamus, wanda zai koma kungiyar daga Bayern a karshen kakar wasa ta bana.
Dan wasan mai shekaru 26 ya amince da kwantiragin shekaru hudu a filin wasa Signal Iduna Park, bayan da ya yanke shawarar kin tsawaita kwantiraginsa da Bayern, wanda zai kare a karshen 2021-22.
Koyaya, Hainer ya nuna shakku kan shawarar da Sule ya yanke na zabar abokan hamayyar Bundesliga, maimakon tayin da za a iya samu daga gasar Premier da LaLiga.
“An riga an tattauna da shi a Dortmund, kuma akwai hasashe Real Madrid da Manchester City da wasu na neman sa, amma ban yi tunanin zai zama zabi na farko ba,” Hainer ya shaida wa Bild.