Shugaban ƙasar Azerbaijan ya zargi jami’an Rasha da ɓoye gaskiya kan abin da ya haifar da hatsarin jirgin saman ƙasar da ya auku ranar Laraba, a ƙasar Kazakhstan da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 38.
Ilham Aliyev ya ce an riƙa bayar da wasu dalilai waɗanda ba su kenan ba.
Ya ce a bayyane take cewa jirgin ya faɗo ne bayan da aka harbo shi a sararin samaniyar Rasha a lokacin da yake ƙoƙarin sauka a Chechnya.
A ranar Asabar ne shugaban Rasha, Vladimir Putin ya kira shugaba Aliyev domin neman afuwarsa kan abin da ya kira mummunan iftila’i.
To amma bai bayyana ɗukar alhakin kakkaɓo jirgin ba.