Fadar White House ta ce, shugaba Biden na cikin koshin lafiya bayan ya faɗi a bainar jama’a ana tsaka da taron yaye sojoji a Colorado.
Shugaban ya yi tuntuɓe ne da wata jakar tara kasa sannan ya hantsila.
Mista Biden, mai shekaru 80, ya samu taimako daga jami’an tsaro nan take, sai dai kuma ya warware ya koma kujerarsa da kansa.
Ya shafe sama da sa’a guda yana karrama sojojin a tsaye kafin faruwar al’amarin.
Tsohon Shugaba Trump kenan a Iowa, yake yi masa tsiya cewa tooo ka fadi, to ina fatan ba ka ji rauni ba, amma dai abun naka akwai mamaki.
Shugaba Biden ya sha watsi da masu sukar cewa ya tsufa da sake neman wa’adi na biyu na mulkin Amurka.
Kuri’ar jin ra’ayi ta baya-bayan nan na nuna cewa Amurkawa da dama na nuna damuwa kan yawan shekarunsa.


