Fadar gwamnatin Amurka ta ce, Shugaba Biden na samun sauki daga cutar koronar da ya kamu da ita.
A ranar Alhamis ne aka tabbatar da cewa sugaban ya kamu da cutar bayan gwajin da aka yi ya nuna hakan. A cewar BBC.
Ya yi kokarin karfafa wa mutane gwiwa a yayin taronsa da manyan masu bashi shawara a kan tattalin arziki inda ya ce yana samun sauki sosai.
Muryar shugaban ta yi kasa sosai ba kamar yadda aka saba jinsa ba, sannan yana fama da tari sosai.
Sakatariyar yada labaran fadar gwamnatin Amurkan ta bayyana cewa yanayin zafin jikinsa ya ragu kuma an bayyana abubuwan da ke damunsa da suka hada da zubar majina daga hancinsa da kuma gajiya sannan yana fama da matsalar numfashi, to amma dai numfashinsa da bugun jininsa duk sun kasance dai dai.