Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya kai ziyara Masallacin Manzon Allah da ƙabarinsa a Madina.
Shafin Haramain Shrifain ya wallafa hotunan shugaban a Masallacin Manzon Allah a ranar Asabar.
Ya kuma yi Sallah a Rauda a cikin Masallacin Manzon Allah (SAW), wurin Annabi ya ce, ya na daga cikin dausayin Aljannah.