fidelitybank

Shugaban ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya rasu

Date:

Shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, Sheikh Khalifa bin Zayed ya rasu a ranar Juma’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar WAM ya ruwaito.

WAM ya ce shugaban ya rasu ne yana da shekara 73 a duniya. In ji BBC.

Tuni kasar ta sanar da makokin kwana 40 inda za a sassauta tutar kasar tun daga ranar Juma’ar 13 ga watan Mayun 2022.

Sannan ta dakatar da aiki a ma’aikatu da hukumomin ƙasar har tsawon kwana uku.

Sheikh Khalifa shi ne sarkin Masarautar Abu Dhabi kuma shugaban ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

A ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasar, mataimakin shugaban ƙasa kuma firimiya Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum, Sarkin Dubai ne zai zama muƙaddashin shugaban ƙasa.

Amma majalisar tarayya, wadda ta ƙunshi shugabannin masarautun ƙasar bakwai za ta yi wani taro a cikin kwana 30 masu zuwa don zaɓar sabon shugaba.

An haifi Sheikh Khalifa a shekarar 1948, kuma ba a faye ganinsa a bainar jama’a ba tun shekarar 2014 da ya gamu da ciwon zuciya.

Tun a lokacin ƙaninsa da suke uba ɗaya kuma yarima mai jiran gadon masarautar Abu Dhabi Mohammed bin Zayed, da aka fi sani da MbZ, wanda babban abokin Amurka ne, shi ke tafiyar da al’amuran ƙasar.

www.legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp