Shugaban Pakistan ya rushe majalisar ƙasar a wani yunƙuri na gudanar da zaɓe da wuri, bayan yunƙurin tsige Firaminista Imran Khan.
An ɗauki matakin ne bayan kakakin majalisar ya yi watsi da buƙatar jefa ƙuri’ar yanke ƙauna kan Imran Khan, wadda aka kyautata zaton ba zai tsallake ba.
Mista Khan ya yi iƙirarin cewa Amurka ce ke jagorantar manaƙisar cire shi saboda sukar manufofinta na ƙasashen waje da yake yi da matakan da yake ɗauka.
Amurka ta musanta zargin sannan ‘yan adawa sun hofintar da batun.
Imran Khan ya kai ziyara Rasha don ganawa da Shugaba Putin yayin da Rashar ke tsaka da kai hare-hare a Ukraine. Ya kuma sha sukar Amurka kan shirinta na “yaƙi da ta’addanci”.