Shugaban sojojin ƙasar Gabon, Janar Brice Oligui Nguema, ya ɗauki wasu matakai da nufin tsuke bakin aljuhun gwamnati a mummunan halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki.
Ya yanke shawarar yin watsi da albashinsa a matsayinsa na “Shugaban ƙasar”, kuma zai karbi albashi ne kawai a matsayinsa na shugaban rundunar tsaron ƙasar, muƙaminsa na da kafin ya hamɓarar da Ali Bongo.
Mai magana da yawun kakakin gwamnatin rikon kwarya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a gidan talabijin na kasar a daren jiya, Larabar.
Rundunar sojin ta kuma sanar da rage alawus-alawus ɗin ‘yan majalisar, da dai sauran matakan da aka dauka na haɗa kuɗaden jama’a da kuma rage kudaden da jihar ke kashewa.


