fidelitybank

Shirin Idon Mikiya: SERAP za ta daukin matakin shari’a a kan Buhari

Date:

Ƙungiyar yaki da rashawa ta SERAPta ce za ta ɗauki matakin shari’a a kan hukumar kula da kafofin yada labarai ta ƙasa (NBC) idan ba ta janye tarar Naira miliyan 5 da ta sanya wa gidan rediyon Vision FM ba da ke Abuja wato cikin awa 24.

A cewar BBC, hukumar ta NBC ta ci tarar gidan rediyon kuma ta dakatar da wani shirinsu mai suna Idon Mikiya na tsawon wata 6, saboda tattaunawar da suka yi kan tsawaita wa’adin Rufai Abubakar, shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta kasa wato National Intelligence Agency (NIA).

NBC ta rubuta wa hukumar Vision FM don sanar da su dokokin yaɗa labarai na Najeriya da suka karya da kuma dakatar da shirin na ‘idon Mikiya’.

Da take mayar da martani ranar Laraba, SERAP ta bayyana matakin na NBC da cewa “ya saba wa kundun tsarin mulki kuma ya saɓa wa doka”, sannan ta yi barazanar kai karar su gaban kotu tare da gwamnatin tarayya idan har ba su ɗage dakatarwar ba da kuma janye kudin tarar nan da awa 24.

“Wannan matakin da gwamnatin Buhari da NBC suka dauka, wani yunƙuri ne na hukumomin ƙasar wajen rufe bakin kafofin yada labarai masu zaman kansu tare da ‘yancin faɗar ra’ayi,” a cewar SERAP cikin wata sanarwa da ta wallafa a Facebook.

“Dole ne gwamnatin ta janye dakatarwar ta kuma bi kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da kuma nauyin da ke kan kasashe don girmamawa da kare hakkin ‘yancin fadin albarkacin baki da samun damar bayanai da kuma yancin yada labarai.

“Wannan wata gazawa ce ga gwamnatin Najeriya wajen kare ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma ba wa kafofofin yada labarai masu zaman kansu damar gudanar da ayyokansu a kasar.”

vanguardnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp