fidelitybank

Shi ma shugaban EFCC a bincike shi – Matawalle

Date:

Bayan da hukumar EFCC ta fitar da sanarwa cewa, ta na binciken gwamnan jihar Zamfara Mohammed Bello Matawalle, kan zargin wawure kudin jihar fiye da Naira biliyan 70, gwamnan ya zargi shugaban hukumar Abdurrasheed Bawa da tafka almundahana iri-iri.

A cikin wata hira da BBC, gwamnan ya kalubalanci Bawa da ya sauka daga kan kujerarsa ya bayar da damar a bincike shi ya ga irin abubuwan da za a bankado.

Gwamna Matawalle ya ce “Bincike gaskiya ne, ba a hana a yi bincike ba, amma kuma ya kamata binciken ya zamo na kowa da kowa, don bai kamata a ce komai sai dai a ambaci gwamna ba, ai ba gwamna ne kadai ke da asusun ajiya ba.”

Ya ce, “Kamar yadda shugaban EFCC ya ce ya tanadi takardu na gwamnoni, to muna so ya nuna wa duniya takardu na wadanda yake aiki tare da su, sannan shi kansa ya kamata ya rubuta wa kansa takarda don a bincike shi saboda akwai zarge-zarge masu dumbin yawa a kansa.”

Gwamnan na Zamfara, ya ce “Akwai shaidu da dama wadanda idan ya sauka za a fito da su a gwada wa duniya cewa shi ba mai gaskiya ba ne.”

Ya ce ‘’ Ya sauka ya gani duk wadanda ke da wata shaida a kansa za su kawo a cikin lokaci kalilan.”

Gwamna Matawalle, ya ce “Akwai abin da shi shugaban EFCC ya san ya yi tsakaninsa da ni, ya san abin da ya roka ban bashi ba a kan haka ya sani gaba.”

Sai dai ita ma hukumar ta EFCC ta kalubalanci gwamnan jihar Zamfarar, Bello Matawalle kan cewa idan yana da hujja a kan cewar shugabanta, Abdulrasheed Bawa na da hannu a ayyukan rashawa to ya kai kara wajen ‘yan sanda.

A lokacin da BBC ta tuntubi shugaban hukumar, Malam Abdulrasheed Bawa, ya ce ai babu wani ɗan’adama da yake 100 bisa 100 a duniya.

Ya ce ‘’Amma dai gwargwadon hali wadannan maganganu da gwamna Matawalle yake yi, wane ya yi kaza, ai sai ya fadi.”

Shugaban na EFCC ya ce, ‘’Idan ya san akwai wani gwamna ko minista da ya yi wani abu ya zo ya kawo, idan kuma ya ga cewa ni na yi wani abu ai akwai ‘yan sanda da wuraren da zai iya rubuta kara sai ya kai idan ya so sai a bincike ni, in ya so sai a gano wanda ke da gaskiya.”

An dai shiga takun saka tsakanin gwamnan da EFCC ne bayan da hukumar ta ce ta aike da goron gayyata ga wasu gwamnoni da za su sauka a karshen watannan domin ta bincike su.

Daga cikin gwamnonin har da gwamnan na Zamfara Mohammed Bello Matawalle, inda ake zargin sa kan badaƙalar kuɗi sama da Naira biliyan 70.

nigerian 
news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp