A ranar Laraba ne mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bar Najeriya domin wakiltar shugaba Bola Tinubu a taron shugabannin kasashen G77 na kasar Sin da za a yi birnin Havana na kasar Cuba, wanda zai gudana daga ranar 15 zuwa 17 ga watan Satumba.
Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa, Olusola Abiola, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce, Shettima zai bi sahun sauran shugabannin duniya ciki har da babban sakataren MDD Antonio Gutteres a wajen taron.
Ya ce taron zai tattauna batutuwan ci gaban da mambobin kungiyar ke fuskanta, musamman daga kudancin duniya.
“Babban taron zai duba hanyoyin da za a bi wajen tunkarar kalubalen da ke fuskantar ci gaban kasashe mambobin kungiyar da ke amfani da kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire don bunkasa ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.
“Har ila yau, Shettima, a gefen taron, zai gudanar da tarukan kasashen biyu tare da sauran shugabannin kasashen duniya, domin inganta huldar kasuwanci da zuba jari a Najeriya, bisa tsarin diflomasiyyar bunkasa tattalin arziki na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu,” in ji shi.
Abiola ya ce, shugaban kasar Cuba Miguel DÃaz-Canel ne zai karbi bakuncin taron na Havana a matsayinsa na shugaban G77.
Taken taron shi ne “Kalubalen Ci gaba na Yanzu: Matsayin Kimiyya, Fasaha da ƘirÆ™ira.”
Ya tunatar da cewa, Najeriya ta kasance memba a kungiyar G77 da kasashe masu tasowa 77 suka kafa a shekarar 1964.
Ya kara da cewa, “Kungiyar, gamayyar kasashe masu tasowa 134 da kashi 80 cikin 100 na al’ummar duniya, na da burin inganta muradun tattalin arzikin mambobinta tare da samar da ingantacciyar damar yin shawarwari tare a Majalisar Dinkin Duniya.”
Ya ce Shettima zai samu rakiyar ministan noma da raya karkara, Abubakar Kyari, da takwaransa na kere-kere, kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, da babban sakataren ma’aikatar harkokin waje, Mista Adamu Lamuwa.


