Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima zai jagoranci tawagar ƙasar da za ta wakilci shugaba Bola Tinubu a wajen taron ƙasashe renon Ingila wato CHOGM 2024.
Shettima zai bi sahun Sarki Charles na Ingila da sauran shugabannin ƙasashen duniya daga mambobi 56 a taron wanda shi ne irinsa na farko da za a yi a Apia, da ke tsibirin Samoa daga 21 zuwa 26 na watan Oktoba.
Wata sanarwa da mai taimakawa Shettima kan harkokin yaɗa labarai Stanley Nkwocha, ya fitar, ta ce shugabannin da za su halarci taron za su mayar da hankali kan “Manufar samar da makoma ɗaya kuma mai kyau tsakanin mambobin ƙasashe.”
Taken taron na bana zai mayar da hankali kan yadda mambobin ƙasashen na renon Ingila za su karfafa gwiwar juna wajen samar da ci gaba a wannan lokaci.
Sanarwar ta ƙara da cewa Najeriya da sauran ƙasashe za su kuma zaɓi sabon sakatare-janar na ƙasashen na renon Ingila yayin taron.
Ana sa ran mataimakin shugaban ƙasar zai yi amfani da damar wajen janyo hankalin masu zuba jari zuwa Najeriya.