Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa Afrika ta Kudu domin wakiltan shugaba Bola Tinubu a taron shugabannin ƙasashen BRICS karo na 15 da za a yi.
Shettima zai bi sahun sauran shugabannin siyasa da ƴan kasuwa a faɗin duniya domin halartar taron a Afrika ta Kudu wanda zai gudana daga 22 ga watan Agusta zuwa 24.
Taron zai tattauna ne kan batutuwan da suka shafi kasuwanci, saukaka zuba jari, samun ci gaba, kirkire-kirkire da kuma garanbawul na yadda ake shugabanci a faɗin duniya.
Har ila yau, taron zai duba batun ci gaba da tallafawa ƙasashen Afrika da kuma kudancin duniya.
Manyan shugabanni da za s halarci taron sun haɗa da Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, Shugaba Xi Jinping na China, Shugaban Brazil, Luiz da Silva da kuma Firaministan Indiya Narendra Modi.