fidelitybank

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Date:

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban taron jami’ar ne Shugaba Tinubu zai zaɓi wanda zai zama mataimakinsa a zaɓen 2027.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Daily Trust a ranar Alhamis.

A baya-bayan nan, rashin jituwa na neman ɓullowa a APC kan wanda zai yi wa Tinubu mataimaki, bayan da gwamnonin APC suka amince da shugaban ƙasar a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a 2027.

A ƙarshen mako ne dai aka kusa bai wa hamata iska a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na shiyyar arewa maso gabas, bayan da wasu ƴan jam’iyyar suka zargi wasu jagorin jam’iyyar da rashin ambatar sunan Kashim Shettima a lokacin da suke jawabin amince wa da Tinubu a matsayin ɗan takarar.

To sai dai tun bayan faruwar lamarin, ba a ji ta bakin fadar shugaban ƙasar ba, lamarin da ya sa wasu ke ganin akwai shirin janye Kashim ɗin daga takarar 2027.

To amma Bayo Onanuga ya musanta wannan zargi yana mai cewa lokaci ne bai yi ba.

“A tsarin takarar shugaban ƙasa, ana fara tsayar da ɗan takara, daga baya sai a zaɓi wanda zai zama mataimakinsa. Haka aka yi lokacin Buhari, an fara tsayar da shi, daga baya ya zaɓi mataimakinsa. Ba a yin su duka lokaci guda,” in ji Onanuga.

A lokacin da yake gwamnan Legas dai, sau kusan uku Tinubu yana sauya mataimaki, abin da ya sa wasu ke ganin zai yi amfani da wancan salo a wannan karon.

To amma Onanuga ya ce, wannan hasashen mutane ne kawai.

“Wannan hasashe ne kawai. Eh, lokacin yana gwamna akwai wasu matsaloli. A wa’adin farko, shi da mataimakiyarsa Kofo ba su jitu ba, hakan ya sa ta bar aiki. Femi Pedro ne ya maye gurbinta. A wa’adinsa na biyu kuma ya ci gaba da aiki da Pedro, sai dai daga baya Pedro ya sauya sheƙa saboda yana so ya tsaya takarar gwamna, wannan ne dalilin barinsa.” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Don haka, ba daidai ba ne a ce Tinubu yana da ɗabi’ar sauya mataimakansa.

the sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mutane 12 sun mutu a wani hatsari a Kano – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta...

Masarutar Rano ta haramta aurar da Yaran da ba su kammala karatun Firamare ba

Masarautar Rano a Kano ta haramta cire yarinya daga...

Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai

Matatar man Dangote za ta fara jigilar mai kyauta...

An sassata rikicin da aka shafe shekaru 30 kan Masallacin Sharada da Islamiyya

Tsohon dan takarar gwamnan Kano, Malam Sha’aban Ibrahim Sharada,...

Duk da kalubalen ‘yan siyasa a Kano mun shirya a zaben cike gurbi – INEC

Kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) reshen jihar...

Barau ya jagorancin gangamin zaben cike gurbi a Kano

Barau ya samu rakiyar Karamin Ministan Gidaje da Raya...

Gwamnatin Kano ta kara fadada shirin matasa 

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya sake,...

An kaiwa Malamin addini hari a Kano bayan an jikatasu da Matarsa

Wani malamin addinin Musulunci, Malam Kabir Idris, da matarsa...

Kotun Kano ta daure wata Mata da ake zargin ta tsafe su

Kotun Majistiri mai lamba 7 da ke Nomansland, ƙarƙashin...

Dalibi ya kashe kansa a cikin Jami’a

Hukumar jami'ar Obafemi Awolowo da ke jihar Osun, sun...

Gobara na cigaba da lakume wasu yankunan Turai

Gobarar daji na ci gaba da ruruwa a sassan...

An kama Fursunoni 7 da suka tsere daga gidan kurkukun jihar Nasarawa

Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya ta ce...
X whatsapp