Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya ƙadammar da shirin gina rukunin gidaje da makarantu da asibitoci da aka yi wa laƙabi da Pulako a garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna.
Yanki ne da sojojin ƙasar suka kai wa hari ta sama bisa kuskure a bara, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Wakilin BBC ya ce, tuni aka kusa kammala masallaci a garin tare da cibiyar koyar da sana’o’i, waɗanda mataimakin shugaban ƙasar ya buɗe a lokacin bikin.

Gwaman Kaduna Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta kashe fiye da naira miliyan 270 domin tallafa wa al’umomin garin na Tudun Biri tun bayan faruwar iftila’in na bara.

Taron ya samu halartar gwamnan jihar jigawa, da wakilan gwamnonin jihohin Kano da Katsina, da wasu ‘yan majalisar dattawa da na wakilai, da sauran manyan baƙi.