Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya yi wa wasu daga cikin iyalan marigayi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta’aziyya a birnin Landan.
Mataimakin shugaban ƙasar ya samu rakiyar shugaban mai’aikatan fadar Gwamnatin Najeriya, Femi Gbajabiamila.
Kashim Shettima ya isar da gaisuwar ne ga maiɗakin mamacin A’isha Buhari da kuma ɗan’uwansa Mamman Daura.
Sauran jami’an gwamnati da ke Landan domin rasuwar tsohon shugaban ƙasar su ne ministan harkokin waje Yusuf Tuggar, da Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum.
Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025 a wani asibiti da ke birnin Landan bayan fama da jinya.