fidelitybank

Shettima ya yi fatali da shugabar jam’iyyar Birtaniya

Date:

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya soki sabuwar zaɓabɓiyar ƴar shugabar jam’iyyar Conservative a Birtaniya, Kemi Badenoch saboda kaskantar da Najeriya.

Shettima ya bayyana haka ne ranar Litinin a taron tattaunawa kan hijira karo na 10 da aka yi a Abuja.

Mataimakin shugaban Najeriyar ya ce “Muna alfahari da kasancewar Kemi Badenoch a matsayin shugabar jam’iyyar Conservative a Birtaniya, duk da kaskantar da ƙasarta ta asali da ta ke yi.”

“Tana da damar bayyana ra’ayinta a kan koma mene ne, kai har ma idan tana son cire Kemi a cikin sunanta ma za ta iya, to amma ba wai hakan ba zai rage wa Najeriya matsayinta na kasancewa ƙasar baƙar fata mafi shahara ba.”

Ya ce, “Idan ka lura duk inda ka samu baƙar fata uku to ko shakka babu za ka ga ɗaya daga cikinsu ɗan Najeriya ne.”

Daga nan ya jaddada ƙoƙarin gwamnati na kare hakkin ƴan ci-rani da kuma taya su murna a kodayaushe saboda irin ci gaba da ma gudunmawar da suke bayar wa wajen ciyar da ƙasa gaba.

A 2022, Badenoch, wato a lokacin da ta ke a matsayin ƴar majalisar dokokin Birtaniya daga Najeriya wadda kuma ake ganin za ta iya zama Firaiministar Birtaniya wata rana, ta zargi ƴan siyasar Najeriya da amfani da kuɗin al’umma don biyan buƙatun kansu.

Bayan zaɓarta a masatyin shugabar jam’iyyar Conservative a watan Nuwambar 2024, shugabar hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ta ce hukumarta ta yi ta tuntuɓar Badenoch, to amma babu wata alama ta nuna cewa ta samu sakon hukumar.

daily sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp