Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya tafi ƙasar Gabon domin halartar bikin rantsar da zaɓaɓɓan shugaban ƙasar, Brice Clotaire Oligui Nguema.
Shettima zai wakilci shugaban Najeriya Bola Tinubu ne a taron bikin, wanda a yanzu haka yake ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar Katsina da ke arewacin ƙasar.
Nguema ya lashe zaɓen ƙasar ne da aka yi a watan Afrilun da ya gabata, bayan ya yi watanni yana mulkin riƙon-ƙwarya.
A wata sanarwar da mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce, “Mataimakin shugaban ƙasar koma Najeriya bayan bikin rantsuwar.”