An gudanar da addu’o’i na musamman don neman gafara ga marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke garin Daura.
Taron addu’ar na zuwa ne bayan addu’ar uku da aka gudanar jiya a Daura a gaban tawagar wakilan gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.
Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya faɗa wa BBC cewa cikin waɗanda suka halarci taron addu’o’in har da tsohon Shugaban Ƙasar Benin Thomas Boni Yayi.
Haka nan, akwai gwamnoni da ministoci da suka hallara a gidan tsohon shugaban.
Nan gaba a yau Shugaba Bola Tinubu zai jagoranci wasu addu’o’in da kuma zaman majalisar zartarwa a Abuja.