A safiyar yau Litinin ne mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya isa birnin Landan domin raka gawar marigayi shugaba Muhammadu Buhari da ya rasu a wani asibiti da ke birnin a jiya Lahadi bayan jinya zuwa Najeriya.
Mataimakin shugaban ƙasar ya isa ne tare da rakiyar shugaban ma’aikatan fadar gwamnati Femi Gbajabiamila.
Sun kuma sami tarba daga Ministan harkokin waje Yusuf Tuggar, da Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum a filin jirgin.
Ana sa ran za su dawo Najeriya a yau domin jana’izar tsohon shugaban ƙasar.