fidelitybank

Shekaru 85 da haihuwa: Obasanjo ya zura ƙwallaye biyu a raga wanda ya lashe kofi

Date:

A wani bangare na bukukuwan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo murnar cik shekaru 85 a duniya, an gudanar da wani wasan kwallon kafa a ranar Juma’a a dakin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL), dake Abeokuta, jihar Ogun.

Obasanjo shi ne kyaftin din kungiyar OOPL, wanda suka fafata da tawagar gwamnatin jihar Ogun karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Noimot Salako-Oyedele.

A lokacin wasan kwallon kafa, Obasanjo ya zura kwallaye biyu daga cikin hudun da aka zura a ragar kungiyar Ogun, inda ya ci biyu a raga.

Da yake magana da manema labarai bayan kammala wasan, Obasanjo ya godewa Allah da ya samu lafiya duk da shekarunsa.

Tsohon shugaban kasar ya shawarci kowa da kowa, musamman ma dattawa, da su dage wajen motsa jiki da gwajin lafiya da hulɗar zamantakewa. Wadannan, in ji shi, su ne sirrin da ke tattare da iyawarsa da lafiyarsa, in ji Daily Post.


Da yake tsokaci game da wasan kwallon kafar, mataimakin gwamnan Ogun ya ce, “A wani bangare na bikin murnar cikar dattijon kasarmu, mai girma Cif Olusegun Obasanjo, cika shekaru 85 da haihuwa, na jagoranci tawagar jihar Ogunbabwasan mutane 5 da ’yan kungiyar OOPL, da na zama kyaftin.

“An yi wasan ne da Baba ya zura kwallaye da dama da kansa. Allah ya nuna mana duka mu sake yin bikin tare da Baba a shekara mai zuwa cikin koshin lafiya.”

tribune

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp