fidelitybank

Shekaru 40 na sashin jarida: Sarkin Kano ya gargaɗi ɗalibai su zama jakadu na gari

Date:

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran manyan baki sun yi kira ga ’ya’yan kungiyar tsofaffin daliban jami’ar Bayero na ɓangaren koyon aikin jarida Mass Communication Association (BUMCAA), da su ci gaba da bayar da goyon baya ga ci gaban sashen da na cibiyar.

Mai martaba Aminu Ado Bayero, wanda kuma ya kammala karatunsa na digiri na biyu a fannin sadarwa na Mass Communication, ajin 1984, ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar a Kano, a wata lacca da kungiyar BUMCAA ta shirya, domin bikin cika shekaru 40 da kafuwar zangon farko.

Ya ce, “Ya na da kyau mu ga yadda za mu ci gaba da taimaka wa ɗaliban mu, bisa iyawarmu. Ya kamata mu kuma taimaka wa masu karamin karfi a cikin al’umma,” inji shi.

Sarkin ya bukaci dalibai da tsofaffin daliban da su ci gaba da zama jakadu nagari a duk inda suka samu kansu.

A nasa jawabin, mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya taya sashen murnar nasarar da aka samu.

nigerianewstoday

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...
X whatsapp