fidelitybank

Shekaru 3 cif da mataimakin shugaban kasa ya tsallake rijiya da baya

Date:

Shekaru uku cif da mataimakin shugaban kasa, Farfaesa Yemi Osibanjo, ya tsallake rijiya da baya, bayan da wani jirgi mai saukar Ungulu ya yi hatsari a garin Kabba na jihar Kogi.

Hadarin, wanda da ya faru ne a ranar 2 ga watan Fabrairu a lokacin da Farfesa Yemi Osibanjo, ke tafiya yakin neman zaben 2019.

Osinbajo, yayin da ya ke mayar da martani kan lamarin, a shekarar 2019, ya ce, za a iya sanyawa ranar a matsayin ‘ranar bakin ciki’ idan lamarin ya lankwame rayukan su.

“Da an tuna da ni a matsayin ranar bakin ciki, saboda hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar 2 ga Fabrairu, 2019, wanda ya hada ni da wasu goma sha daya a ciki.

“Amma ina farin ciki kuma mun gode wa Allah da ya zama ranar nasara da godiya,” in ji Osibanjo.

Kasancewar lokacin yakin neman zabe, wasu ‘yan siyasa, musamman ‘yan jam’iyyun adawa sun yi murna da wannan lamari, inda suka yi zargin cewa hukunci ne na gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

world news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp