Tsohon gwamnan jihar Kano kuma a halin yanzu Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Shekarau ya sauya sheka ne a zauren majalisar dattijai yayin zaman majalisar a ranar Laraba.
Ya kasance dan jamâiyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, kafin ya sauya sheka.
A baya dai ya fice daga jamâiyyar All Progressives Congress zuwa NNPP.