Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano, Sadiq Wali, ya yi zargin cewa yakin neman zabe da ake yi wa Mallam Ibrahim Shekarau wani shiri ne na haifar da rikici a cikin jam’iyyar da kuma raunana ta gabanin zaben gwamna da za a yi a karshen mako mai zuwa.
Shekarau ya sauya sheka daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP zuwa PDP a daidai lokacin da ake tunkarar zaben 2023 a karshen shekarar da ta gabata.
Da yake magana a yayin wani taron manema labarai a Kano a daren ranar Alhamis, Wali ya ce babu gaskiya cikin jita-jitar da ake yadawa na cewa Shekarau yana aiki da dan takarar APC a zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 11 ga Maris.
Dan takarar gwamnan na PDP ya jaddada cewa babu shakka zai iya cewa Shekarau yana yi masa aiki domin samun nasarar PDP a jihar.
A cewar Wali, wannan jita-jita ta samo asali ne daga shirun da Shekarau ya yi a rikicin PDP a Kano, domin an yi shari’ar a kotu.
Ya ce: “Ba gaskiya ba ne. Me Shekarau zai amfana da shi idan ya yi wa Gawuna aiki a yanzu? Zan iya fada muku babu shakka Mallam Ibrahim Shekarau ba shi da wata matsala da takara ta. Wai a ce Shekarau yana aiki a karkashin kasa don yakar takarata.
“Kawai dai Shekarau ya yanke shawarar yin shiru a rikicin PDP a matakin jiha, saboda ana shari’ar a kotu. A matsayinsa na mutum mai mutunta doka da dimokuradiyya, bai kamata ya yi magana a kan karar da ke gaban kotu ba. Amma ni a ra’ayina, ba gaskiya ba ne cewa Shekarau yana yi wa APC aiki.”