Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan’adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana shekara ta 2023, a matsayin mafi tashin hankali ga aikin jarida, saboda shekara ce da aka kashe ‘yan jarida da ma’aikatan yaɗa labarai har 71 a faɗin duniya.
Babban Kwamishinan Kare Haƙƙin Ɗan’adam na Majalisar Ɗinkin Duniya, Volker Turk ya ce a shekarar an kuma ɗaure ‘yan jarida har 320, adadi mafi yawa da aka taɓa samu.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wani jawabin da ya gabatar, albarkacin Ranar Tunawa da ‘Yancin ‘Yan Jarida ta 2024, wadda ake gudanarwa a yau Juma’a.
Ya ce idan yana tunawa da aƙidojin aikin jarida, yana tunawa ne da amana da gaskiya da tsare ƙima. Yana tuna ɗumbin ɗaiɗaikun mutanen da ba su da tsoro, kuma suna da ƙundumbalar yin tambaya.
Mutane ne masu yin ƙuru wajen ƙalubalantar gwamnati da sanya rayuwarsu cikin kasada wajen tattaro bayanan aika-aikar da aka tafka da cin hanci da wani laifi, da kuma tsayawa haiƙan wajen yaƙi da zalunci.
A cewarsa, idan muka rasa ɗan jarida, mun yi asarar idanuwanmu da kunnuwanmu. Mun rasa murya ga mutanen da ba a jin amonsu.
Haƙiƙanin gaskiya ma dai, mun rasa mai kare haƙƙin ɗan’adam.
Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya, an ɓullo da ita ne don tunawa da aƙidar gaskiya da kuma kare mutanen da ke aiki da ƙwarin gwiwa don bankaɗo gaskiya.