Masu haƙar kayan tarihi a Isra’ila sun ce an gano wasu sulalla tun na ƙarni na bakwai, wato shekara kusan 1,400 da suka wuve kenan a ɓoye a cikin wata rijiya.
An samu sulallan masu nauyin giram 170 ne a wata rijiya Hermon a yankin Banias da aka ɓoye a wajen a shekara ta 635, kamar yadda ƙwararru suka ƙiyasta.
Sun ce sulallan sun ƙara bayyana ƙarshen Daular Byzantine ta Gabas a yankin.
Daular Rumawa ɗin ita ce rabin Daular Rumawa a gabas, wacce ta yi zamani fiye da shekara 1,000.
“Muna ganin kamar mai su ne ya ɓoye su a yayin da ake cikin barazanar yaƙi, da fatan wata rana zai koma ya kwashe kayansa,” in ji Yoav Lerer, shugaban tonon kayan tarihin. In ji BBC.