Shekara biyu da ta gabata jirgin sama mai saukar ungulu da ke dauke ministan wasanni na Iran Hamid Sajjadi, ya yi hadari a lardin Kermano.
Mista Sajjadi tare da mutane da dama da ke cikin jirgin da suka hada da Ismail Ahmadi, mai ba wa ministan shawara da babban daraktan a ofishin ministan sn rasu a hadarin.
Tawagar tana komawa Tehran ne daga Bafat a cikin jirgin saman mai saukar ungulu na kungiyar agaji ta.
Binciken da hukumomi suka yi ya nuna cewa kuskuren mutum ne ya haddasa hadarin ba wata matsala ta na’ura ko injin jirgin ba. In ji BBC.
Wata biyu kafin wannan hadarin shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent Society a Iran ya ce jiragen sama masu saukar ungulu na agaji na kungiyar guda 10, ba sa aiki saboda rashin kudaden gyara su.