Shugabannin ƙananan hukumomi a jihar Kano, na cigaba da gudanar da bukukuwa tare da shirya taron liyafar shekara guda a karagar mulki.
Wasu daga cikin shugabannin na bayyana irin ayyukan da su ka yiwa ƙananan hukumomin su a shafukan sadarwa na zamani.
Jihar Kano dai na ƙananan hukumomi 44 wanda kuma Jami’yyar APC mai mulki ce ke jan ragamar kowacce ƙaramar hukuma.
A cikin watan Janairun shekarar 2021 ne dai aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi ƙarƙashin shugaban hukumar zaben jihar, Farfesa Garba Ibrahim Sheka, inda aka rantsar da su a cikin watan Fabrairun shekarar.
Haka kuma a lokacin zaɓen Jam’iyyar PDP tsagin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ke hamayya ba ta shiga zaben ba saboda, a cewarta, kudin fom din da aka sayarwa ƴan takara ya wuce kima.