Wani matashi dan shekara 25 da aka fi sani da Elisha Tari, ya bayyana dalilin da ya sa ya jefe ’ya’yansa biyu har lahira a gidansa.
Idan dai ba a manta ba rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke Elisha da laifin jefewa ‘ya’yansa biyu masu shekaru 3 da 5 da jifa har lahira.
Yayin da ake gabatar da shi a ranar Litinin, wanda ake zargin ya amsa cewa yana da matsalar tabin hankali kuma an taba daure shi da sarka a wani lokaci da ya wuce.
“Ina shan hemp na Indiya, ina shan barasa, kuma ina shakar snuff. Ba na shan tramadol ko wasu kwayoyi masu tsauri,” inji shi.


